An jinjinawa kotun daukaka kara a Masar

'Yan matan Masar a kurkuku
Image caption 'Yan matan Masar a kurkuku

An saki wasu 'yan mata su ashirin da daya a Masar, bayan da wata kotun daukaka kara ta soke hukuncin daurin da aka yanke masu , bisa laifin shiga zanga zangar masu kishin Islamar dake goyon bayan hambararren shugaban kasar, Muhammad Mursi.

Hukuncin dauri na farko ya girgiza jama'a a ciki da wajen Masar.

Kotun a birnin Iskandiyya ta mayar da daurin shekaru sha daya da aka yanke a kan mata sha hudu, zuwa na gyaran hali na shekara guda.

Su kuma wasu 'yan matan bakwai da a da aka yanke ma hukuncin zama a gidan kangararun yara, yanzu an jingine hukuncin.