Za a yi wa Mandela janaizar girmamawa

Image caption Za ayi jana'izar Mandela

Shugaba Jacob Zuma ya sanar da cewa za a yi jana'izar girmamawa ga marigayi Nelson Mandela a nar Lahadi Sha biyar ga wannan watan Disamba bayan an shafe fiye da mako guda ana jimamin mutuwarsa.

Shugaba Zuma yace za a yiwa Mr Mandela jana'izar girmamawa a a kauyensu Qunu da ke yammacin Cape.

Jacob Zuma ya ce "mu hada karfi da karfe dan ganin an gudanar da jana'izar girmamawa ga babban da ga Afrika ta kudu, kuma uba ga al'umar kasar nan.

An ayyana gobe lahadi da ranar addu'a ta musamman a kasar Africa ta kudu, haka kuma za a gudanar da irin wannan addu'a a talata mai zuwa a Filin wasa da ke wajen birnin Johannesburg.

Za kuma a ajiye gawar Mr Mandela na kwanaki 3 dan yi masa gani na karshe a Pretoria kafin a binne shi.

Karin bayani