Tunawa da Nelson Mandela

Nelson Mandela
Image caption Nelson Mandela

Al'ummar kasar Afrika ta kudu sun shiga addu'oi na kasa da za a gudanar a yau don tunawa da abubuwan da Nelson Mandela ya yi a duniya

Shugaba Jacob Zuma ya yi kira ga mutane a duk fadin kasar da su halarci dandalin tarukka da Majami'u da Masallatai da sauran wuraren ibada don tunawa da tsohon Shugaban kasar.

Iyalin Mr Mandela sun ce sun ji dadi da sakonnin da suke cigaba da samu na ta'aziyya da kuma tallafin da suke cigaba da samu daga gwamnati da mutane daga sassa dabam-dabam na duniya.

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta ce za a ratsa da gawar Nelson Mandela ta titunan birnin Pretoria, babban birnin kasar, kwanaki uku a jere, cikin mako mai kamawa, domin ba jama'a damar yi masa ban kwana.

Wani ministan gwamnati, Collins Chabane ya ce daga ranar Laraba za a fara ratsawa da gawa.

Karin bayani