Obama da Michelle za su jana'izar Mandela

Image caption Obama da matarsa za su jana'izar Mandela

Fadar White House ta sanar da cewa shugaba Obama da mai dakinsa Michelle za su tafi kasar Afrika ta Kudu a mako mai zuwa domin halartar jana'izar Mr Mandela.

Ana dai ci gaba da nuna alhinin mutuwar jagoran kwatowa bakaken fatar Afrika ta kudu 'yanci.

Shugaban kasar Ghana John Mahama ya shaidawa BBC cewa Mr Mandela gawurtaccen shugaba ne ga 'yan Afrika baki daya.

Shima shugaban Syria Bashar-al-asssad ya ce rayuwar Nelson Mandela abar koyi ce ga masu fafutukar 'yanci kuma darasi ga azzalumai.

Karin bayani