Mataimakin shugaban kasar Sudan ya yi murabus

Omar Al Bashir
Image caption Shugaba Omar Al bashir

Shugaba Omar Al-Bashir ya sanar da murabus din mataimakin Shugaban kasar Sudan na farko Ali Taha, a wani mataki na garambawul a gwamnatin kasar.

Rahotani sun ruwaito Shugaba Al-Bashir yana cewa Mr Taha ya ba da kafa ne ta shigowar sabbin jinin 'yan siyasa a fagen mulki.

Shugaba Al bashir ya kuma ce babu wani bambanci tsakaninsa da Mr Taha wanda yake daya ne daga cikin jiga-jigan mutanen da suka yi juyin mulkin da ya dora Al-Bashir a kan karagar mulki.

Masu aiko mana labarai sun ce ga alama garambawul din na da nufin sanyaya ran mutanen da suka yi zanga-zanga bayan karin kudin man fetur watan Satumba .