Ana kokarin bunkasa kasuwanci a duniya

Ministocin cinikayya a Bali
Image caption Taron Ministocin cinikayya a Bali

Ministocin cinikayya na kasashen duniya sun cimma wata yarjejeniya dake da manufar bunkasa kasuwanci a kasashen duniya.

Yarjejeniyar da aka cimma a karshen taron da suka yi a Bali na kasar Indonesia, zata saukaka hanyoyin cinikayya ta kuma sa kasashe matalauta su samu saukin sayar da kayayyakinsu.

Yarjejeniya ba karamin tasiri zata yi ba a harkar kasuwanci a duk fadin duniya.

Zata bude wata sabuwar hanyar kasuwanci tare da samarwa kamfanoni saukin tura kayayyakinsu ta kan iyakoki.

Masana tattalin arzuki sun kiyasce cewa yarjejeniyar zata habaka tattalin arzuki duniya da sama da pam biliyan biyar a shekara da kuma samar da ayyuka miliyan 20.