Dakarun Faransa a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Dakarun Faransa a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
Image caption Dakarun Faransa a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

An kara samun bayanai game da irin mummunar ta'asar da ake tafkawa a jamhuriyar Tsakiyar Afrika, inda dakarun Faransa ke kokarin dawo da zaman lafiya, bayan rikicin addinin da yayi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.

Wani wakilin BBC a garin Bossangoa ya bayyana abubuwan da ya gani masu tayar da hankali.

Ya ziyarci gidan wani limami, inda mutane da yawa suka je suka nemi mafaka, amma daga baya wasu 'yan banga kiristoci suka je suka karkashe su.

Can kuma a Bangui, babban birnin kasar, kungiyoyin agaji sun ce wasu mayaka da galibinsu na kungiyar 'yan tawayen Seleka ce ta Musulmi, sun afka wani asibiti, inda suka kashe wasu kiristoci tara da ke jinyar raunukan da aka yi masu.

Shugaban jamhuriyar tsakiyar Afrikar, Michel Djotodia ya amsa cewa ba duka mayakan ne ke saurarensa ba.

Yanzu haka dai dakarun Faransa sun karade sassan arewaci da yammacin kasar domin tallafawa dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen Afrika, wadanda ke ta kokarin shawo kan rikici mai nasaba da addini da ya barke.

Shugaban kungiyar agaji ta Save the Children- wanda ya ziyarci wani yanki na jamhuriyar tsakiyar Afrikar kusa da kan iyaka da Kamaru, ya ce a yanzu akwai dubban daruruwan mutane dake kwana a filin Allah Ta'alah.