Ana ci gaba da rikicin addini a CAR

Cental African Republic
Image caption Dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Afrka ta tsakiya

Ana ci gaba da samun karin bayanai a kan mummunar ta'asar da ake tafkawa a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, inda dakarun Faransa ke kokarin farfado da zaman lafiya.

Wakilin BBC a garin Bossangoa dake arewacin kasar ya ziyarci gidan wani limami, inda mutane da yawa suka nemi mafaka.

Sai dai daga baya wasu 'yan banga kiristoci suka je suka karkashe su.

A Bangui kuma, babban birnin kasar, kungiyoyin agaji sun ce wasu mayaka da galibinsu na kungiyar 'yan tawayen Seleka ne ta Musulmi, sun afka wani asibiti, inda suka kashe wasu kiristoci akalla tara.

Rikicin adinin da ya barke ranar Alhamis din data gabata ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane .

Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku daga ranar lahadi sakamakon kashe-kashen da aka yi .