An kashe mutane 9 a kasar Iraki

Iraq
Image caption Fira Ministan Iraq Al Maliki

Wasu 'yan bindiga dadi a kasar Iraqi sun kai hari a kan shaguna da dama da ake sayar da barasa a Bagadaza babban birnin kasar .

'Yan bindigar sun kuma kashe a kalla mutane 9 tare da raunata wasu da dama a yankin Waziristan dake arewacin kasar.

An yi imanin cewa mutanen da lamarin ya fi shafa Kurdawa ne tsiraru.

Ba a san kowane ne ke da alhakin kai hare-haren ba.

Sai dai a can baya 'yan kishin Islama sun rika kai hare-hare a irin wadannan shaguna wadanda mabiya wasu addinan ne 'yan tsiraru ne ke tafiyar da su.