Taron addu'oin tunawa da Nelson Mandela

Addu'o iga Nelson Mandela a wata Majami'a a Afirka ta Kudu
Image caption Addu'o iga Nelson Mandela a wata Majami'a a Afirka ta Kudu

Hukumomin Afrika ta Kudu sun ce shugabanin kasashe kimanin 60 ne zasu halarci taron addu'o'in da za a yi wa Nelson Mandela a makon nan.

Za a yi jana'izar tsohon shugaban kasar ne a ranar Lahadi mai zuwa, a kauyen Qunu, dake yankin Eastern Cape, inda ya taso.

Akwai wani taron addu'o'in da za a yi a wani filin wasa dake birnin Johannesburg, da za a nuna kai tsaye, a sauran wuraren taruwar jama'a.

A yau miliyoyin 'yan Afrika ta Kudu, sun yi addu'o'in tunawa da Mr Mandela a ranar da aka kebe domin haka.

Iyalan Mandelan sun ce sun ji dadi da sakonnin da suke cigaba da samu na ta'aziyya da kuma tallafin da suke cigaba da samu daga gwamnati da mutane daga sassa dabam-dabam na duniya.

Wani mai magana da yawun iyalin ya ce, irin yadda duniya ke nuna juyayi ga mutuwar ta Mr Mandela ya nuna cewar, shi, ba wai dan kasar Afrika ta Kudu ba ne kadai, mutum ne na kowa a duniya.

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta ce za a ratsa da gawar Nelson Mandela ta titunan birnin Pretoria, babban birnin kasar, kwanaki uku a jere cikin mako mai kamawa, domin ba jama'a damar yi masa ban kwana.