Faransa za ta kwace makaman mayakan CAR

Sojin Faransa a CAR
Image caption Dakarun Faransa na sintiri a Bangui, babban birnin CAR

Dakarun Faransa za su fara karbe makaman mayakan jamhuriyar Afrika ta tsakiya (CAR) daga wannan Litinin din, ko da kuwa da karfin tsiya ne hakan ta kama, in ji kasar Faransa.

Faransa ta tura dakaru 1,600 zuwa CAR bayan da rikicin da ya barke a kasar ya hallaka mutane 400.

Jagoran 'yan tawaye Michel Djotodia ya kwace mulki a watan Maris, kuma 'yan bindiga wadanda mafi yawansu tsofaffin 'yan tawaye ne sun karbe iko a kasar.

Yanzu haka dai dakarun Faransa na sintiri a titunan Bangui, babban birnin kasar, bayanda majalisar dinkin duniya ta amince da daukar matakan kawo karshen rikicin.

Faransa ta kuma ce kungiyar AU za ta kara yawan dakarunta daga 2,500 zuwa 6,000.