Kotu ta wanke 'yan adawa a Kuwait

'Yan adawar Kuwait
Image caption 'Yan adawar Kuwait na murnar wanke su da kotu ta yi.

Wani alkali a Kuwait ya wanke 'yan adawa 70 ciki har da tsofaffin 'yan majalisa tara daga zargin da ya danganci mamaye zauren majalisar dokokin kasar a shekarar 2011.

Lauyoyinsu sun bayyana cewa wadanda ake zargin ba su da niyyar aikata laifi, amma suna zanga-zangar adawa da Pirai ministan wancan lokacin ne, Sheikh Nasser Al-Sabah bisa zargin cin rashawa.

Sheikh Nasser ya yi murabus makonni biyu bayan zanga-zangar inda aka gudanar da sabon zabe.

Tsawon shekaru biyun da suka gabata, an sha yin zanga-zangar adawa da gwamnatin Kuwait.