Taron addu'o'in girmama Nelson Mandela

Nelson Mandela
Image caption Marigayi Nelson Mandela

Dubban 'yan kasar Afrika ta kudu sun shiga layi suna kokarin shiga dandalin wasanni na Soweto wurinda za a yi addu'oi na musamman na girmama Nelson Mandela nan gaba a yau.

Mafi rinjayensu sun shafe daren jiya ne a sansanin da suka yi gaban dandalin wasannin don samun shiga, duk kuwa da ruwan saman da aka sheka.

Shugabanni daga kasashen duniya da suka hada da Amurka da Cuba za su hadu da su a taron addu'ar.

Sun tashi zuwa birnin na Johannesburg ne don yin bankwanan karshe ga tsohon Shugaban kasar.

Tsare marigayin da aka yi a gidan Yari da gwagwarmayarsa ta siyasa sun sanya shi ya zamo wani gwarzo a duniya.

Za a nuna addu'oin ta talabijin kai-tsaye ga dubban mutanen dake kallo a sauran wasu dandalin wasannin ukku dake Johannesburg da kuma sauran miliyoyin mutane a duniya.