Tambuwal ya zargi Jonathan kan rashawa

Hon Aminu Waziri Tambuwal
Bayanan hoto,

Hon Aminu Waziri Tambuwal

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal ya yi zargin cewa wasu take-taken shugaban kasar na taimakawa wajen habakar matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya.

Kakakin ya ce Majalisar Wakilan kasar ta sha yunkurin yaki da cin hanci a lokuta daban-daban, amma bangaren zartarwa na sanyaya mata gwiwa.

Ya ce akwai manyan matsaloli na cin hanci da rashawa da suka faru a harkar tallafin man fetur da Majalisar wakilan ta binciko makudan kudade da wasu suka sace.

Da kuma wasu batutuwa da suka shafi hukumar dake kula da hada-hadar kudi na kasar wadda Majalisar ta bada shawarar sauke shugabar hukumar daga mukaminta.

Aminu Tambuwal ya ce maimakon gwamnati ta yi amfani da sakamakon binciken da Majalisar tayi , kwamiti ta kafa kuma kawo yanzu shuru ake ji.