Rasha ta rushe kamfanin dillancin labarai

Vladimir Putin
Image caption Shugaban Rasha, Vladimir Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rushe kamfanin dillancin labarai na RIA Novosti mallakar gwamnatin kasar.

Mr. Putin ya ce za'a maye gurbin kamfanin da wata sabuwar hukuma mai suna Russia Today, karkashin jagorancin Dimitry Kiselev, daya daga cikin 'yan-gani-kashenin fadar shugaban kasa wanda ya yi kaurin suna bisa ra'ayin 'yan mazan jiya.

Kawo yanzu babu wani cikakken bayani game da dalilin rushe RIA Novosti, amma dai a shekarun baya bayan nan kamfanin na kokarin adalci a rahotanninsa inda ya kan baiwa 'yan adawa damar bayyana ra'ayoyinsu.

Haka kuma an rufe gidan rediyon Voice of Russia mallakar gwamnatin.