Dakaru na tsoma baki a rikicin Ukraine

Sojjin Ukraine
Image caption 'Yan sandar kwantar da tarzoma sun fara lalata tantunan da masu zanga-zangar suka kafa a tsakiyar Kiev, babban birnin kasar.

Jami'an tsaro a Ukraine sun fara daukar matakan takura wa 'yan adawa da kuma tarwatsa masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnati.

Daya daga cikin manyan jam'iyyuun adawar kasar, Fatherland, ta ce jami'an tsaro sun shiga Sakatariyarta, tare da kwashe na'urorin komfuta dake wurin.

Hakazalika, wata jami'iyyar adawar ta ce an rufe shafinta na Intanat.

A halin da ake ciki kuma, 'yan sandar kwantar da tarzoma sun fara lalata tantunan da masu zanga-zangar suka kafa a tsakiyar Kiev, babban birnin kasar.

Tun farko shugaba Viktor Yanukovich mai goyon bayan Rasha, ya ce a shirye yake ya tattauna da 'yan adawa.

Masu zanga-zangar dai suna bukatar gwamnati ta yi murabus, sannan a gudanar da sabon zabe, a kuma karfafa hulda da kungiyar Tarayyar Turai.