Faransa ta kare matakin da ta dauka a CAR

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Image caption Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Shugaban kasar Faransa Francoise Holland ya kare matakin da kasarsa ta dauka na tura soji zuwa Jumhuriyar Afrika ta tsakiya.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne bayan kisan sojojin Faransar biyu a wani fadan da aka gwabza a Bangui, babban birnin kasar.

An kashe sojojin Fransar ne a kokarinsu na kwace makamai daga hannun sojin sa kai na kasar da kuma dakatar da fadan addini da aka fara a makon da ya wuce.

Mr Holland ya ce tura sojojin Faransa 1,600 da aka yi, ya zama wajibi don kawar da kisan kiyashi.

Faransa ta tura dakarunta ne domin kwance damarar mayakan Musulmai da Kirista da basa ga miciji, wadanda ake zargin sun kashe daruruwan mutane.

Karin bayani