Jonathan ya baiwa jihohin PDP kudi - APC

Image caption Shugaba Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo

Babbar jam'iyyar adawa a Nigeria-APC ta yi zargin cewar shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan ya baiwa jihohi 17 da jam'iyyar PDP ke mulki naira biliyan biyu-biyu.

Sakataren yada labarai na APC, Alhaji Lai Muhammed wanda ya yi wannan zargin, ya ce Mr Jonathan ya bada wadannan kudaden a boye duk da cewar akwai wasu jihohin dake fama da matsalolin muhalli.

Jihohin da aka baiwa kudaden sun hada da Abia da Anambra da Bauchi da Bayelsa da Benue da Cross River da Gombe da Kaduna da Katsina da kuma Kebbi.

A cewar APC din ana shirin amfani da kudaden ne wajen yakin neman zaben Shugaba Jonathan a shekara ta 2015.

Ana shi bangaren,mai baiwa Shugaba Jonathan shawara ta kan harkokin siyasa, Ali Ahmed Gulak ya bayyana cewar zargin bai da tushe kuma shugaban kasar ba mutum bane da yake nuna wariya a tsakanin al'ummar Nigeria.

Gulak ya kara da cewar kafin a baiwa wata jiha irin wadannan kudade, a kan gudanar da bincike domin a gano girman wannan matsala,sannan kuma akwai ka'idoji da ake bi wajen bada wadannan kudade.

Karin bayani