Ana taron tuna Mandela a Johannesburg

Taron tuna Mandela
Image caption Dubunnan mutane ne ke halartar taron tuna Mandela.

Dubunnan mutane na cigaba da tururuwa zuwa wani filin kwallo dake Johannesburg inda ake gudanar da taron tunawa da Nelson Mandela.

Shugaban Amurka Barak Obama, shugaban Cuba Raul Castro da Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon za su gabatar da jawabai tare da hudu daga cikin jikokin Mr Mandela.

Karfe 09:00 GMT aka fara taron a filin mai daukar mutane dubu 95 amma har yanzu mutane na cigaba da kwarara.

Tsohon shugaban kasar na Afrika ta kudu ya mutu ne ranar Alhamis ya na da shekaru 95.

An shirya bukukuwa da dama na tunawa da Mandela kafin jana'izarsa ranar Lahadi.