Takaddama kan baitulmalin Nijar

Tandja Mamadou
Image caption Tsohon shugaban kasar Nijar Tandja Mamadou

Hukumomin jamhuriyar Nijar sun musanta ikirarin da tsohon shugaban kasa Tandja Mamadou ya yi cewa ya bar CFA biliyan 400 a baitulmalin kasar lokacin da sojoji suka yi masa juyin mulki ranar 18 ga Fabarairun 2010.

Babban darektan baitulmalin kasar, Malam Suleiman Zulkarnaini ya ce CFA biliyan 43 kawai shugaba Tandja ya bari a lalitar gwamnati.

Sai dai magoya bayan tsohon shugaban kasar sun ce su na nan kan bakansu.

Sun kuma ce a shirye su ke tsohon shugaban kasar ya bayyana gaban alkali domin bayar da haske kan maganar idan hukuma na bukata.