'Yan sandan Ukraine sun afkawa masu zanga-zanga

Ukraine
Image caption 'yan sanda a dandalin 'yanci na Ukraine

Mutumin da ya fito a matsayin jagoran 'yan adawa a Ukraine, Vitali Klischko, ya ce amfani da karfin da ake a kan masu zanga zanga ya rufe kofar sasantawa.

Ya ce,"mun shirya sa matsin lamba kan gwamnati dan a saki mutanan da ake tsare da su a gidan yari kuma mu gurfanar da masu laifi mu kuma wanna tin da ta jefa mu cikin halin da ake ciki a yau."

Tsohon dan danban ya zargi gwamnati da kin san a sasanta, duk kuwa da sanarwar da shugaban kasar ya sa a shafin yanar gizonsa ta gayyatarsu zaman sasantawa.

Shugaba Vikto Yunakovych ya ce kada mutanen dake neman ya yi murabus su kai ga shimfida sharruda.

Tun da gwamnatin Ukraine ta ki sa hannu a kan wata yarjejeniya tare da tarayyar Turai a watan jiya ake ta zanga zanga a Qib babban birnin kasar.

Tun farko dai daruruwan 'yan sandan Ukraine sun kutsa kai a sansanin da masu zanga-zanga suka kafa a dandalin 'yanci dake tsakiyar Kiev, babban birnin kasar.