'Yan luwadi da madigo na kokawa a India

Image caption 'Yan luwadi da madigo a na rajin neman 'yanci a India.

Masu rajin kare hakkin 'yan luwadi da madigo a Indiya na yin kakkausar suka ga hukuncin da kotun kolin kasar ta zartar wanda ke tabbatar da dokar da ta haramta luwadi da madigo, bayan da ta soke wani hukunci da karamar kotu ta zartar.

Al'umomin Hindu, da Musulmi, da Kirista sun koka da hukuncin karamar kotun, inda suka ce wajibi ne a dauki luwadi da madigo a matsayin ayyukan laifi.

Kungiyar Amnesty International ta ce hukuncin koma baya ne ga hakkin al'umma na daidaito da kuma mutuntawa.

Kotun kolin ta ce majalisar dokoki ce kawai za ta iya sauya dokar, sai dai Ministan shari'a na India Kapil Sibal bai bayyana ko gwamnatin za ta dauki matakin sauya dokar ba.