India ta tabbatar da haramta luwadi

Image caption 'Yan luwadi da madigo na neman 'yancinsu a India

Kotun kolin India ta tabbatar da dokar da ta haramta luwadi da madigo.

Kotun kolin ta soke wani hukunci ne da babbar kotun Delhi ta yi a 2009 inda ta halatta luwadi.

A cewar kotun kolin majalisar dokoki ce kawai ke da damar yin doka game da lamarin.

Sashe na 377 na kundin dokokin Indina da aka kafa shekaru 153 da suka wuce lokacin mulkin mallaka, jima'i tsakanin jinsi guda "abu ne da ya sabawa hankali" kuma akwai hukunci daurin shekaru 10 ga duk wanda ya aikata.

Al'ummar India dai na daukar luwadi da madigo a matsayin abin kyama.