Jonathan na horas da 'yan bindiga -Obasanjo

Image caption Cif Obasanjo ya ce shugaba Jonathan na horas da 'yan bindiga

Tsohon shugaban Nigeria, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi zargin cewa shugaban kasa, Goodluck Jonathan, yana horas da 'yan bindiga-dadi domin kashe abokan hamayyarsa na siyasa.

Cif Obansanjo ya kara da cewa shugaba Jonathan yana yunkurin wargaza Nigeria.

A wata wasika mai shafi 18, Cif Obasanjo ya ce Mista Jonathan ya yi alkawarin cewa mulki zango daya zai yi sannan ya bai wa 'yan arewa amma dukkan take-takensa sun nuna cewa ba shi da niyyar cika alkawarin da ya dauka.

Mista Obasanjo ya yi zargin cewa shugaba Jonathan ya kewaye kansa da 'yan kabilarsa, don haka ne ma 'yan kasar ke yi masa kallon shugaban wani bangare na Nigeria.

Zargin ba shi da tushe

Sai dai a martanin da ya yi, mai bai wa shugaban kasar shawara a harkar watsa labarai, Reuben Abati, ya ce bayyana wasikar bai dace ba, yana mai cewa wata hanya ce ta harzuka 'yan Nigeria.

Ya kara da cewa shugaba Jonathan da kansa zai mayar da martani a kan wasikar da Abati ya bayyana da cewa ta kunshi ''zarge-zargen da ba su da tushe balle makama''.

Karin bayani