An rage mutuwar yara a Mali

Ibrahim Boubacar Keita
Image caption Mali ta samu wannan nasara duk da rikicin da take fama da shi

A kasar Mali wani gagarumin shirin kula da lafiya ya samu nasarar rage yawan mutuwar yara fiye da yadda aka yi tsammani.

A tsawon shekaru uku ma'aikatan lafiya sun yi nasarar rage yawan mace mace daga kashi 15 cikin dari zuwa kashi 1 cikin dari a wani kauye da ke wajen babban birnin kasar Bamako.

Ma'aikatan lafiyar sun ce a karkashin shirin suna ziyartar gidaje ne inda suke yi wa yara rigakafin kamuwa da cututtuka kamar su zazzabin cizon sauro da gudawa da cutar sanyi ta nimoniya, maimakon su jira sai yara sun kamu da cuta a yi musu magani.

Wani ayarin masana daga Amurka ne ya wallafa sakamakon shirin.

Dr Ari Johnson daga jami'ar California, ya sheda wa BBC cewa shirin wani gagarumin sauyi ne a fannin kula da lafiya.