An fara bikin 'yancin kai a Kenya

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta wanda a wannan ranar mahaifinsa Jomo ya kasance shugaban kasar na mulkin kai na farko, shi ne ya jagoranci bikin.

Al'ummar kasar Kenya sun fara bukukuwan mako guda na zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar daga Birtania, tsohuwar uwar gijiyarta ta mulkin mallaka.

An gudanar da wani biki a lambun Uhuru da ke babban birnin kasar, Nairobi.

Inda aka sauke tutar Birtaniya tare da daga tutar Kenya, kamar dai yadda aka yi a wurin ranar 12 ga watan Disamba na 1963.

Hakan na nuna samun 'yancin kan kasar daga Birtaniya.

Cuncurundon al'ummar kasar sanye da tufafi masu launin tutar kasar sun rika kada tutar kasar, sannan kuma an yi wasan wuta a dandalin.