An rasa Naira biliyan 48 na man Nigeria

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Nijeriya kenan Goodluck Jonathan

A Nijeriya, Kungiyar SERAP mai yaki da cin hanci da tabbatar da kawo daidaito a tsakanin al'ummar kasar ta bukaci gwamnati ta bayyana dalilan rashin shigar da wasu kudade sama da Naira biliyan 48 wadanda aka samu wajen sayar da albarkantun man fetur cikin baitulmalin gwamnatin tarayya.

Kungiyar na neman shugaba Goodluck Jonathan da ya tursasawa kamfanin man fetur na kasar wato NNPC ya bayyana masa abinda aka yi da kudaden a shekara ta 2013.

Duk da gwamnatin ta na ikirarin cewa ta na yaki da cin hanci da rashawa, kungiyoyi da masu rajin yaki da cin hancin da rashawa a ciki da wajen Nigeria, suna ganin shirye-shiryen gwamnatin ba su yin wani tasiri.

Majalisar dokokin kasar ma a kwana-kwanan nan, sai da ta yi zargin cewa, duk wani yunkuri da ta yi na yaki da cin hancin, gwamnati ce ke sukurkutar da maganar.

Karin bayani