Hoton su Obama ya ja kace-nace

Cameron, Schmidt, Obama da Mitchell
Image caption Ashe matan manya ma na kishi?

Hoton da Pirai ministar Denmark, Helle Thorning-Schmidt ta dauka a wayarta tare da takwaranta na Britaniya David Cameron da shugaban kasar Amurka Barak Obama a taron tuna Nelson Mandela ya haddasa kace-nace a jaridun Birtaniya.

Jaridar Daily Mail cewa ta yi lalle Michel Obama ba ta ji dadin wannan hoto ba, inda Sun da Mirror suka ce wannan rashin girmamawa ne ga marigayi Mandela.

Haka ma ma'abota shafukan Facebook da Twitter sun yi ta yamadidi da hotunan suna tofa albarkacin bakinsu.

Hotunan dai na nuna Helle Thorning-Schmidt ne a tsakiyar su Cameron da Obama yayin da Michelle Obama ke gefe fuska a turbune.

Daya hoton kuma na nuna Michelle Obama ta sauya wurin zama da mijinta inda ta shiga tsakaninsa da Pirai ministan Denmark, abinda ya sa masu bayyana ra'ayinsu ke cewa ashe matan manya ma na kishi?