An dakatar da tallafawa 'yan tawayen Syria

Image caption Amurka da Birtaniya sun dakatar da tallafawa 'yan tawaye a Syria

Amurka da Birtaniya sun dakatar da shirin bada kwarya-kwaryar taimako ga 'yan adawar dake yaki da gwamnatin Syria a arewacin kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da wani rahoto ya ce masu kishin Islama sun kwace sansanonin 'yan tawayen da kasashen Yamma ke marawa baya.

Taimakon dai wadanda ba na makamai bane sun hada da kamar tabaron gani da dare da kuma kayan sadarwa.

Sai dai Amurka ta ce ba za 'a daina kai agajin gaggawa ga wadanda yakin ya rutsa da su ba.

Mummunan halin da al'ummar yankin ke ciki na dada ta'azzara.

Karin bayani