'Yan tawayen M23 sun dena yaki

'Yan tawayen kungiyar M23 da suka mika wuya
Image caption A watan da ya wuce 'yan tawayen suka mika wuya bayan wasu hare hare da sojojin Congo suka kaddamar musu.

Gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar 'yan tawaye ta M23, wadda ta zubar da makamanta.

Wani mai magana da yawun gwamnatin ya ce 'yan tawayen sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a babban birnin kasar Kenya Nairobi, inda suka tabbatar da kawo karshen tawayensu.

Gwamnatin Kinshasan ta sanya hannu a wata yarjejeniyar ta daban inda ta amince ta sanya mayakan kungiyar 'yan tawayen cikin sojojin kasar kuma ta yafe wa dukkanninsu in ban da wadanda aka zarga da aikata laifukan yaki.

Da dama daga cikin mayakan kungiyar tawayen ta M23 sun taba aiki a rundunar soji ta Congo, bayan da aka sanya su cikin rundunar sakamakon yarjejeniyar da aka taba kullawa bayan wani tawayen da aka taba yi tun da farko a gabashin kasar.