An rataye Abdul Kader Mullah a Bangladesh

Image caption Abdul Kader Mullah

An aiwatar da hukuncin kisa kan shugaban 'yan adawa na masu kishin Islama na Bangladesh, Abdul Kader Mullah.

An sameshi da laifin cin zarafin bil adama a lokacin yakin kwatar 'yancin kai daga kasar Pakistan a shekarar 1971.

Da farko an dakatar da aiwatar da hukuncin kisan bayan da ya daukaka kara, amma daga bisani kotun kolin kasar ta Bangladesh ta amince a kan aiwatar da hukuncin kisan a kan Mullah din.

Rikici ya barke a birne uku dake gabashin kasar wato Chittagong, Sylhet da Rajshahi a yayinda aka tsaurara matakan tsaro daukacin Bangladesh.

Wannan ne karon farko da aka aiwatar da hukuncin kisa a Bangladesh tun bayan kafa kotun musamman kan laifuffukan yaki.

Karin bayani