Dogayen layuka don kallon gawar Mandela

Image caption Mutane na jira don su kalli gawar Mandela

Dubban 'yan Afrika ta Kudu suna ta bin dogayen layukan don kallon gawar tsohon Shugaban kasar, Nelson Mandela a rana biyu.

A yanzu haka gawar Nelson Mandela na kwance cikin ginin Union Buildings na Pretoria, inda aka rantsar da shi shugaban kasar Afrika ta Kudu bakar fata na farko a 1994.

Matarsa Graca Machel da Shugaban kasa, Jacob Zuma na daga cikin mutanen farko da suka yi wa gawar bankwana.

An dauko akwatin gawar da aka nade da tutar kasar ne a keken doki inda 'yan sanda suka yi mata rakiya kan babura yayinda jiragen helikopta ke shawagi kan su.

A ranar Lahadi ne kuma za'a binne gawar a kauyen Qunu dake Afrika ta Kudu.

Karin bayani