Boko Haram ce ta kai hari a Maiduguri

Abubakar Shekau da mukarrabansa
Bayanan hoto,

Abubakar Shekau da mukarrabansa

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce kungiyarsu ce ta kaddamar da hare-hare a kan cibiyoyin jami'an tsaro a Maiduguri a ranar 2 ga wannan watan.

A bidiyon wanda aka rabawa manema labarai, Shekau ya ce sun samu galaba a kan jami'an tsaron Nigeria kuma za su ci gaba da kai hare-hare.

A harin da 'yan Boko Haram suka kai a sansanin sojin sama dake Maiduguri, sun lalata jiragen yaki biyar tare da bankawa gine-gine wuta, tare da yin barna a barikin sojoji na 333.

Jami'an tsaron Nigeria sun ce sun kashe 'yan Boko Haram 25 a lokacin harin, amma Shekau a sabon bidiyon ya ce mutanensu bakwai ne suka mutu, sannan su kuma sun kashe sojoji da dama.

A bidiyon wanda aka nuna gine-gine da jiragen sama na ci da wuta, Shekau ya yi gargadin cewa "Kada ku yi tunani zamu tsaya a Maiduguri, gobe za ku ganmu a cikin Amurka."