Syria: Amnesty ta soki kungiyar EU

Image caption 'Yan gudun hijirar Syria

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta soki Tarayyar Turai kan abinda ta kira da yadda bata nuna tausayawa ba ga matsalar 'yan gudun hijirar Syria.

A cikin wani rahoto Amnesty ta bayyana irin matsaloli da hadurran da mutanen da ke kokarin isa turai kan fuskanta ciki har da tsare su na tsahon lokaci.

Amnesty ta soki shugabannin Turai kan karancin adadin mutanen da za ta tsugunar.

Russell Hargrave na kungiyar bada agaji ga 'yan gudun hijira da ke Burtaniya mai suna Asylum Aid ya ce sakamakon wannan binciken daidai yake da abinda kungiyarsa take gani.

Yace "Irin yadda Tarayyar Turai ta nuna rashin tausayawa akan 'yan Syria bai dace ba ko kadan,kuma kungiyar da nake aiki da ita na ganin haka kowanne lokaci."

Karin bayani