CAR : za a aike da karin dakaru 6000

Image caption Gwamnatin Faransa ta ce ana fuskantar mummunar hatsari

Kungiyar hada kan kasashen Africa ta amince a kara dakarun da za a aika kasar Jamhuriyar Africa ta tsakiya zuwa 6,000.

Kasar dai ta fada cikin rikici tun lokacin da shugaban masu tayar da kayar-baya,Michel Djotodia, ya jagoranci tumbuke shugaban kasar Francois Bozize a watan Maris.

Dakarun kungiyar kasashen Africa na yunkurin mayar da zaman lafiya a kasar, kana su karbe makamai daga hannun masu tayar da kayar-baya wadanda ke rike da akasarin sassan kasar.

Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya yi gargadin cewa Africa ta tsakiya na fuskantar mummunan hatsari.

Le Drian ya je babban birnin kasar, Bangui, ranar Juma'a inda ya gana da dakarun da Faransa ta tura su 1,600, sannan ya tattauna da wadansu jami'an gwamnati.

Karin bayani