Jonathan ya yi wa 'yan arewa alkawari - OBJ

Image caption Obasanjo ya goyi bayan Jonathan a 2015

Tsohon Shugaban Nigeria, Cif Olusegun Obasanjo ya ce ya kamata Shugaba Goodluck Jonathan ya cika alkawarin da ya dauka na yin wa'adin mulki daya tal sannan ya mika wa arewacin kasar.

A wata wasika mai shafi 18, Cif Obasanjo ya ce bisa dukkan alamu take-taken Mr Jonathan sun nuna cewa ba shi da niyyar cika alkawarin da ya dauka.

A cikin wasikar dai tsohon shugaban na Najeriya ya zargi shugaban mai ci yanzu da kokarin ruguza kasar, da haddasa rigimar cikin gida a jam'iyyar PDP mai mulki, da nuna bambancin kabila da bangaranci.

Sai dai tuni fadar shugaba Jonathan ta bayyana wasikar a matsayin mara tushe da rashin madogara da ma rashin kawaici.

A cewar kakakin fadar, Dr Ruben Abati shugaba Jonathan da kansa zai mayar da martani a kan wasikar da ya bayyana da cewa wata hanya ce ta harzuka 'yan Nigeria.

Karin bayani