Polio: An kashe 'yan sanda biyu a Pakistan

Image caption Pakistan da India da Nigeria ne ake samu yara masu cutar shan inna.

'Yan sanda a arewa maso yammacin Pakistan sun ce an harbe jami'anta biyu a kan hanyarsu ta baiwa ma'aikata diga Polio kariya.

An kaiwa mazan hari ne lokacin suna tafiya a kan babur a garin Topi dake da nisan kilomita 100 daga Peshawar.

'Yan Taliban na kallon shirin bada allurar Polio a matsayin wata hanya da kasashen waje ke yi wa kasarsu leken asiri.

Mayaka a Pakistan sun kashe fiye da ma'aikatan bada Polio 12 a cikin shekara guda.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta amsa kai wannan harin.

Karin bayani