Jirgin Turkey ya fara tashi daga Kano

Image caption Jirgin Turkey na farko da ya sauka a Kano, Nigeria.

Kamfanin jirgin saman Turkiyya (Turkish Airlines) ya fara jigilar fasinja daga Kano, Nigeria zuwa birnin Santambul na Turkiyya.

Jirgin, samfurin Boeing 787-800 DELTA mai daukar fasinja 151 ya fara tashi ne a daren Juma'a kuma zai ci gaba da daukar fasinja sau hudu a kowanne mako.

A baya dai gwamnatin jihar Kano ta sha zargin ma'aikatar sufurin jiragen saman Nigeria da yunkurin hana jirage sauka a birnin domin dakile tattalin arzikin yankin.

Sai dai ministar ta musanta hakan.