Jami'an FBI sun yi wa wani gadar-zare

Barak Obama
Image caption Ana zargin Mr Loewen da niyyar kai harin bamabamai a filin jirgin saman Kansas

Hukumomi a Amurka sun kama wani mutum da ya ce yana son ya yi jihadi, bayan da aka yaudare shi a ka ba shi mota da cewa tana dauke da bama bamai da zai tayar a wani filin jirgin sama a Kansas.

Mutumin mai suna Terry Lee Loewen wanda ke aiki a filin jirgin sama na Mid-Continent a Wichita ya fada wannan tarkon ne a wani aiki da hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ta ke yi na shirya gadar zare domin gano masu nufin aikata laifi.

Masu gabatar da kara sun ce jami'an tsaron farin kaya ne suka shirya tare da bai wa mutumin motar dauke da abubuwan da ya dauka bama baman ne a ciki.

Amma sun ce ba wanda ya shiga wani hadari a filin jirgin saman a sanadiyyar shirin.

Babban lauyan gwamnatin Amurka Barry ya ce a karar laifin da aka shigar a kotun tarayya ana zargin Mr Loewen da cewa ya yi watanni yana tsara yadda zai yi amfani da katinsa na shiga filin jirgin saman da motar da ke dauke da bama bamai da zai tayar.