Gawar Mandela ta isa Qunu

Gawar marigayi tsohon shugaban Afurka ta kudu, Nelson Mandela ta isa garin Qunu inda gobe Lahadi za a binne shi, baya an yi kwanaki uku jama'a gallon karshe ga gawarsa.

Mutane da dama ne suka yi tururuwa kan tituna yayin da ake kan hanyar kai gawar Nelson Mandela zuwa garin da yayi yarintarsa wato Qunu.

Dubban mutane ne suke cigaba da fitowa yayin da waucewa da gawar dake cikin akwatin da aka lullube da tutar kasar Afurka ta kudu.

Daga Pretoria jirgin saman ne ya dauko gawar Nelson Mandelan ya sauka a yankin gabashin Cape na Afurka ta kudu.