Ban, ya soki amfani da makamai masu guba

Image caption Za a hukunta wadanda suka ayi amfani da makamai masu guba

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr Ban Ki-moon ya soki amfani da makamai masu guba a rikicin Syria da cewa laifi ne da ya sabawa al'adar dan adam.

Mr Ban, ya bayyana wa babban taron majalisar cewa irin wadannan hare hare sun yi matukar sabawa dokokin kasashen duniya, kuma dole ne a hukunta wadanda su ka aikata su.

Babban Sakataren ya fadi hakan ne a lokacin da yake gabatar da rahoton karshe na masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya.

Masu binciken dai sun tabbatar cewa anyi amfani da makaman masu guba kusan akalla sau biyar, da suka hada da wanda aka tabbatar an kai a kusa da Damascus a watan Agusta wanda a lokacin ya hallaka daruruwan mutane.

Karin bayani