Tarayyar Turai ta dakatar da yarjejeniya da Ukraine

Shugaban Ukraine Yanukovich da Catherine Ashton ta EU
Image caption Shugaban Ukraine Yanukovich da Catherine Ashton ta EU

Kungiyar Tarayyar Turai ta dakatar da ayyukan yarjejeniyar kasuwanci da kasar Ukraine saboda gaza rattaba hannun shugaban kasar Viktor Yanukovych.

A bayyane take cewa matsin lambar da Mr Yanukovych ke samu daga kasar Rasha ne ya sa shi gaza rattaba hannun.

Sai dai Ukraine da Tarayyar din sun ce za su ci gaba da tattaunawa,

Dubannin mutane ne har ila yau ke gudanar da zanga-zanga a birnin Kiev sakamakon gaza rattaba hannun da Mr Yanukovych ya yi.

Ana kuma sa ran magoya bayan gwamnatin kasar za su gudanar da ta su zanga-zangar a kusa.