An binne Nelson Mandela a Qunu

Image caption Shugabanni a duniya sun jinjinawa Nelson Mandela

An binne gawar tsohon shugaban Afrika ta Kudu, Nelson Mandela a kusa da kaburburan 'yan uwansa a kauyen Qunu dake gabashin Cape.

A lokacin bukin dai shugabanni na siyasa dana addinni sun yi jawabai na ban kwana ga gwarzon yaki da wariyar launin fata a duniya.

Matar da ya bari, Graca Machel da Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma na daga cikin wadanda suka halarci wani bangare na bukin wanda 'yan kabilarsa ta Xhosa su ka shirya a kauyen da ya taso a Qunu.

Jana'izar tasa dai za ta kunshi al'adu na hukuma da kuma tsatsibe tsatsibe na kabilarsu , da ya hada da yanka wani bijimin sa.

Kimanin baki dubu biyar ne suka yi wa gawar ban girma na karshe a bikin da aka yi a wata makekiyar rumfa fara da aka kafa a kauyen.

Mr Mandela ya rasu ne a ranar 5 ga watan Disamba yana da shekaru 95.

Karin bayani