Saudiyya: Za a yi wa mai fafutuka bulala 300

Image caption Wasu masu fafutukar kare hakkin bil'adama a Sudiyya

Wata kungiyar kare hakkin bil'adama a Saudi Arabia tace, an yankewa daya daga cikin jami'anta hukuncin zaman gidan kaso na shekaru hudu.

Za a kuma yi masa bulala dari uku.

An same shi ne da laifin yin kiran a wanzar da dimukradiyya a kasar.

Shi dai Omar Al-Saeed shi ne na baya-bayan nan cikin 'yan kungiyar Saudi Civil and Political Rights da aka daure, yayin da hukumomin Saudiyya suke cigaba da yaki da kungiyar.

An kafa kungiyar a shekara ta 2009, kuma tana tsayawa wadanda a ka daure a gidan yarin a Saudiyya da suke cewa, ana danne musu hakkokinsu.