CAR:Kamaru ta aike da kayan abinci

Gwamnatin kasar Kamaru ta fara aika wa 'ya'yanta da ke zaune Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya agaji na abinci da kuma magunguna hade da wasu kayan bukata.

Hakan nan kuma ta fara kwaso wadanda suka nuna bukatar komawa gida.

Ko da yake dai babu wani bayani game da adadin 'yan kasar ta Kamaru da ke zaune a Jumhuriyar Afrikar ta Tsakiya saboda akasarinsu 'yan kasuwa ne da dalibai, ita ma kasar ta Kamaru ta yi asarar mutane biyu a tashin hankalin da ya yi kamari a baya-bayan nan wanda ya haddasa kisan kimanin mutane 400 a cikin kwanaki uku.

Rikicin kasar dai ya yi kamari ne tsakanin musulmai da kiristoci.

Karin bayani