'An kashe sama da mutane 20 a Congo'

Image caption An kashe mata da kananan yara a Kivu

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar dinkin duniya a gabashin Jumhuriyar demokradiyyar Congo ta ce an kashe sama da mutane ashirin wadanda suka kunshi mata da kananan yara a lardin Kivu na arewacin kasar.

Dakarun na Majalisar dinkin duniya sun ce wadanda suka mutu ga alama banbankare su aka yi a ranakun Jumm'a da Asabar da suka wuce a Kauyuka biyu dake kusa da Beni.

Ba'a dai tantance wanda ya yi wannan aika-aikar ba

Amma jagoran dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin duniyar ya ce, duk wanda ya aikata kisan gillar ba ba zai sha ba.

Karin bayani