'Yunkurin juyin mulki a Sudan ta Kudu'

Image caption Salva Kiir ya dora alhaki kan tsohon mataimakinsa

Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya ce dakarunsa sun bankado wani yunkiri na juyin mulki, bayan fadan da aka yi cikin dare a Juba, babban birnin kasar.

Mista Kiir, wanda dan kabilar Dinka ne da ke da rinjaye, ya dora alhakin rikicin a kan magoya bayan tsohon mataimakinsa, Riek Mahar, wanda dan kabilar Nuer ne da ba su da rinjaye.

Mista Kiir ya sa dokar hana fita da daddare a birnin kuma ya ce a yanzu gwamnati ke iko da birnin.

Dakarun kungiyoyin da ba sa ga miciji sun kwashe sa'o'i suna gwabza kazamin fada kuma an ce an kashe mutane.

Karin bayani