Nigeria: ASUU ta janye yajin aiki

Image caption Jami'o'in Nigeria sun dara watanni biyar babu karatu.

Kungiyar malaman jami'o'i ta Nigeria, ASUU, ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni biyar ta na yi domin neman gwamnatin kasar ta inganta ilimin jami'a.

Shugaban kungiyar na kasa Dr Nasiru Fagge ne ya baiyana haka a taron manema labarai da ya gudanar a jami'ar fasaha ta tarayya da ke Minna, jihar Niger (FUT Minna).

Dr Fagge ya ce ASUU ta dakatar da yajin aikin ne bayan cimma matsaya da gwamnatin tarayya da kuma amincewar mambobinta.

An dai sha kai ruwa rana tsakanin gwamnatin da kungiyar ASUU game da yajin aikin inda har gwamnatin ta yi barazanar korar daukacin malaman jami'ar idan su ka gaza komawa bakin aiki kafin wa'adin da ta deba musu, sai dai barazanar ba ta yi tasiri ba.

Ranar 1 ga Yulin da ya gabata ASUU ta shiga yakin da zimmar matsawa gwamnatin Najeriya ta cika alkawurran da ta daukarwa kungiyar a yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2009.