Za'a kara mazabun kansiloli a Nigeria

Zabe a Najeriya
Image caption Bisa doka duk bayan shekaru goma ake sake duba rumfunan zabe

Hukumomi a Nijeriya sun bayyana aniyar nazari kan mazabun kasar domin sake musu iyaka da kuma kirkiro sababbi.

A bisa doka dai duk bayan shekaru 10 ake sake duba mazabu da rumfunan zabe, domin yi masu garambawul ko kirkiro sababbi daidai da bukatun yawan jama'a a yankuna.

A yanzu haka akwai mazabun kansiloli kimanin 9,000 a fadin Nijeriya, yayin da rumfunan zabe kuma suka kai kusan 120,000.

Wannan batu na kirkiro karin rumfunan zabe da mazabun kansiloli dai na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen zabukan kasa baki daya a shekarar 2015.

Fatan 'yan Nijeriya da dama dai shi ne ba wai a tabbatar da karin yankunan zabe kawai ba, a' a, a gudanar da ingantattun zabuka na gari bisa mizanin dimokradiyya na kasa da kasa.