Za a tasa keyar Isa Mu'azu zuwa Nigeria

Image caption Muazu ya ce rayuwarsa na cikin hadari a Nigeria.

Dan Najeriya din nan, Isa Mu'azu, wanda ke neman mafaka a Biritaniya, wanda ya kwashe watanni ukku yana yajin cin abinci don gudun kada a maida shi Najeriyar, bai yi nasara ba a turjiyar a kan fitar da shi daga Birtaniyar.

Wata kotun musamman a kan shige da fici ce ta ce hujjojin Isa Mu'azun ba su da madogara.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Birtaniya ta ce ranar Talata da yamma za a mayar da dan Najeriyar mai shekaru 45 kasarsa.

Shi dai Isa Mu'azu ya nemi mafakar siyasa ce a Birtaniya bisa zargin cewar rayuwar tana cikin hadari idan ya koma Nigeria saboda 'yan Boko Haram za su iya hallaka shi.

Karin bayani